Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Tunusiya Ya Maye Gurbin Ministoci A Wani Gagarumin Sauyi ~ Fadar Shugaban Kasa


Shugaban Tunisiya Kais Saied
Shugaban Tunisiya Kais Saied

Shugaban Tunisiya Kais Saied ya maye gurbin ministoci daban-daban da suka hada da na harkokin waje da na tsaro, fadar shugaban kasar Tunisiya ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafin Facebook ba tare da wani bayani ba ranar Lahadi.

Sauye-sauyen ba zato ba tsammani na maye gurbin ministoci 19 da sakatarorin gwamnati uku, kwanaki kadan bayan Saied ya kori tsohon firaminista.

“A safiyar yau, 25 ga watan Agusta, 2024, shugaban kasar ya yanke shawarar yin sauyi a gwamnati,” in ji sanarwar, ba tare da wani karin bayani ba.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da kasar da ke arewacin Afirka, ke shirin gudanar da zaben shugaban kasa a ranar 6 ga watan Oktoba.

Saied mai shekaru 66, an zabe shi ta hanyar dimokaradiyya a shekarar 2019, amma ya kitsa yunkurin kwace madafun iko a shekarar 2021.

Yanzu yana neman wa'adi na biyu na shugaban kasa a matsayin wani bangare na abin da ya ce “yakin 'yanci da cin gashin kansa” da nufin “kafa sabuwar jamhuriya.”

Sai dai yayin da yake neman takara, a halin yanzu akwai wasu abokan hamayyarsa na siyasa da masu sukar sa a gidan yari ko kuma an gurfanar da su gaban kuliya.

A farkon makon nan ne kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch (HRW) mai sa ido a duniya, ta ce hukumomin Tunisiya sun “gurfanar gaban kuliya, ko yanke hukunci ko kuma daure akalla 'yan takara takwas” a zaben na Oktoba.

Kungiyar ta HRW ta kara da cewa, kasar da ke arewacin Afirka karkashin Saied ta ce "tana shirin gudanar da zaben shugaban kasa a daidai lokacin da ake kara murkushe 'yan adawa da kuma 'yancin fadin albarkacin baki, ba tare da tantance karfin ikon shugaba Saied ba".

A farkon wannan watan, Abir Moussi, wata babbar ‘yar adawar da ke gidan yari tun watan Oktoba, an yanke mata hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari karkashin wata doka ta yada “labaran karya”, kwanaki bayan da aka ce ta mika mata takarar shugaban kasa ta hannun lauyoyinta.

Sauran 'yan takarar da aka daure sun hada da Issam Chebbi, shugaban jam'iyyar Al Joumhouri mai tsatsauran ra'ayi, da Ghazi Chaouchi, shugaban jam'iyyar Social-Democratic Party Democratic Current, wadanda dukkansu ake tsare da su saboda “kulla makirci ga kasa.”

Bayan daure fitattun 'yan adawa da masu fafutuka da dama, hukumomin “Bayan daure mafi yawan ‘yan adawa da masu raji, Tunisiya sun cire kusan dukkanin masu neman takarar shugabancin kasar, lamarin da ya rage yawan kuri'u zuwa wani tsari kawai,” in ji Bassam Khawaja, mataimakin darektan HRW a Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG