‘’To na farko dalilin da yasa shi mai girma Gwamna shi da mataimakin sa yasa suka yi wannan sadaukarwan na kashi 50 na albashin su da alawus-alawus shine ganin halindasu mutanen jihar Kaduna suke ciki, musammam talakkawa harkan kiwon lafiya data ilmi data tsaro da kuma ta zaman takewa da kuma rashin hanyoyi da kuma sauran abubuwa da yakamata ace mutanen jihar Kaduna suna jin dadin su dalilin da yasa aka yi wannan abun Kenan’’.
To kamar nawa yawan albashin shi gwamnan da mataimakin nasa?
‘’Kasan akwai wannan hukumar dake kayyade albashi da kuma alawus- alawus na jamian gwamnati a Najeriya, a halin yanzu da muke Magana ban zaton cewa sun bada adadin ko nawa ne gwamnoni da mataimakan su zasu karba amma dai abu dai mafi muhimmaci shine gwamnan ya fito yace dashi da mataimakin sa sunsadaukar da kashi 50 na albashin su da sauran kudaden shiga nasu kaga wannan ba karamin abu bane tana da tasiri kwarai da gaske’’
Akwai wani batu wanda ake zargi shi gwamna El Rufai ya dauko wasu wadanda ba 'yan jihar ba ya basu mukamai ina gaskiyar wannan lamari yake?.
‘’Ban zaton wadanda suke wadannan maganganun sunyi nazari sosai ko kuma sun duba yanayin wannan abin da suke Magana akai, na farko duk wani mutiumin da yake jihar Kaduna mutumin Najeriya ne kuma mutumin jihar Kaduna ne kuma wadannan mutanen da aka basu wannan matsayin ba wai ba wai fadowa sukayi daga sama ba akace anyi musu wannan matsayin ba a’a, wannan siyasar wadda akayi farkon ta har karshen ta inda ALLAH madaukakin sarki ya bamu nasara dasu akayi uwa dasu aka yi makarbiya ban zatan mutane basu fahinci wannan abun da kyau ba akwai gurguwar fahinta da sauran su.
Mamud Lalo Ne Yayi Hirar