Kaddamar da aikin tono mai a tsakanin jihohin Bauchi da Gombe da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai yi, zai zama daya daga cikin ayyukan da ba za a taba mantawa da su ba a tarihin mulkinsa, daya daga ciki hadimansa, Bashir Ahmad ya ce.
Ahmad ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook a ranar Litinin.
A ranar Talatar nan Buhari zai kaddamar da shirin aikin tono man a jihohin biyu da ke makwabtaka da juna a arewa a maso gabashin Najeriya.
Za a yi bikin kaddamar da aiki a filayen Kolmani, wanda shi za zama aikin tono mai na farko da za a yi a arewacin Najeriya.
Najeriya na da dumbin arzikin mai amma a kudancin kasar.
Rahotanni sun ce filayen Kalmoni da za a kaddamar da aikin, na dauke da arzikin man da yawansa ya haura sama da ganga biliyan daya.
Ana kuma fatan wannan aiki zai bunkasa adadin man da Najeriya take da shi, wanda cikin shekaru goma bai karu ba kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito