Rundunar tsaron hadin guiwa ta JTF dake Maiduguri a Jihar Borno, ta yaba ma matasan nan da aka fi sani da sunan "Civilian JTF" ko kuma Rundunar JTF ta farar hula, a saboda sadaukar da kai da rayukansu da suke yi wajen farautar miyagun mutane dake dauke da makamai.
A cikin wata hira ta musamman da Sashen Hausa na Muryar Amurka, kakakin rundunar, Leftana-kanar Sagir Musa, yace duk da kai musu farmaki da kashe wasunsu da 'yan bindigar Boko Haram suka yi, wadannan matasan sun ci gaba da sadaukar da rayukansu domin tabbatar da cewa an kawar da wannan masifa da ta addabi Maiduguri.
Yace dama dai babu ta yadda za a iya shawo kan wannan lamarin tsaro ba tare da hadin kan jama'a ba, kuma wannan aiki da matasan keyi, karbar addu'ar da suka yi ce ta neman Allah Ya sa jama'a su mike su yaki wannan bala'in.
Yace irin abubuwan da wadannan matasa suka yi, sun taimaka sosai wajen kara karfafa tsaro a Maiduguri da ma Jihar Borno baki daya.
Sai dai kuma Kanar Sagir yayi kira ga matasan da su kula, su daina wuce gona da iri, su rika gudanar da ayyukansu bisa la'akari da dokokin kasa. Yace jama'a su na koke-koke da yawa kan take-taken wadannan matasa, saboda haka akwai bukatar su yi ayyukansu bisa doka.
Ya kuma ce tilas a daina makala musu sunan "JTF" domin wadannan haruffa na jami'an tsaro ne, kuma ba su da makamancinsu na farar hula.
Ga Kanar Sagir Musa da cikakken bayanin wadannan abubuwa.
Rundunar JTF ta yaba ma matasan dake farautar 'yan Boko Haram, amma kuma ta ce tilas ne matasan su daina musgunawa jama'a, su kuma bi dokokin kasa.