Wadanda suka tsallake rijiya da baya sunce an kone wadansu kurmus da ransu jiya asabar a wani harin da aka kai da asuba a kauyen Mamudo dake arewa maso gabashin Najeriya da ake fama da tashe tashen hankali. Wani dalibi yace an tashe shi da bindiga, aka kuma harbeshi aka ji mashi rauni, aka tsinke yatsunshi hudu na dama. Dalibai da dama kuma sun gudu suka shiga jeji, ba a kuma san makomarsu ba.
Makarantar tana yankin da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kafa dokar ta baci ya kuma tura dakaru da nufin shawo kan tada kayar bayan da mayaka ke yi na neman kafa shari’ar Islama.
Sai dai wani mutum da ya rasa ya’yanshi biyu a harin yace babu tsaro a yankin. Yace ‘yan bindiga suna kaiwa makarantu hari kuma ba a kare dalibai duk da sojojin dake ke wurin.
Hukumomi suna kyautata zaton kungiyar Boko Haram ce ta kai harin.
Wakiliyarmu Sa’adatu Mohamad Fawu tayi hira da wani mazaunin garin Mamudo dangane da harin.