Matan sun yi wannan rokon ne a yayin da shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewacin Najeriya, Babangida Aliyu, yake mika gudumawar Naira miliyan 100 ga masu takabar a madadin jihohin arewa, kuma a yayin da gwamnan Jihar Ebonyi shi ma yake mika gudumawar buhu dubu daya na shinkafa ga matan.
Matan sun ce samun hanyar da zasu rika aiki su na ciyar da 'ya'yansu da kula da su, ita ce zata tabbatar da dorewar rayuwarsu na dogon lokaci, maimakon gudumawar da idan ya kare ba su da wata hanyar.
Gwamnan Jihar ta nassarawa, inda wannan abu ya faru, Tanko Almakura, yayi alkawarin za a nazarci dukkan bukatun matan dake takaba da iyalansu kafin a yanke shawarar yadda za a raba musu wannan gudumawa. Haka kuma yace gwamnatinsa zata yi bakin kokarinta na ganin an kula da iyalan mamatan.
Wakiliyarmu Zainab Babaji, ta aiko da cikakken bayani daga Lafia, babban birnin Jihar Nassarawa.