Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiragen yakin Amurka sun hallaka mayakan ISIS 40 a Libya


Sabratha, Libya, birnin da jiragen yaki suka kai hari
Sabratha, Libya, birnin da jiragen yaki suka kai hari

Jiragen saman yakin Amurka sun yi lugudan wuta akan wurin da kungiyar ISIS ke horas da mayakanta dake yammacin Libiya kusa da iyakar kasar da Tunisia kamar yadda wasu jami'an Amurka suka sanar.

Harin na yau Juama'a ya lalata wni gini a garin Sabratha dake yammacin Tripoli a yankin da akan san masu tsatstsauran ra'ayin addini sun yi kakagida.

Jami'an karamar hukumar yankin sun ce akalla mutane 40 suka rasa rayukansu. Wasu jami'an yammacin Turai sun gayawa jaridar New York Times cewa cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai fiye da 30 da suka kasance sabbin dauka shiga kungiyar ta ISIS.

An ji wani jami'ain yammacin Turai yana cewa an auna harin ne kan wani babban jami'in kungiyar dake zaune a kasar Tunisia daga inda yake shirya hari wanda kuma yana da hannu cikin wasu hare hare biyu na ta'adanci da aka yi a bara akasar ta Tunisia.

Amurka dai ta amince ita ta kai har-hare akalla sau biyu a wasu lokutan cikin 'yan watannin nan da suka haddasa kasheshugaban ISIS a Libya a harin watan Nuwamba a garin Derna.

Libya ta fada cikin yamutsi da rikicin siyasa tun lokacin aka hambare Moammar Gadhafi mai mulkin kama karya a shekarar 2011. Kungiyar ISIS tana anfani da rikicin kasar ne ta fadada ayyukanta a arewcin Afirka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG