Galibin kudade da kungiyar take samu daga cinikin mai ne, da aka yi kiyasin tana samun kimanin dala milyan dari biyar, zuwa yanzu daga kasuwannin bayan fage. Haka nan tana samun kudade daga kayan tarihi da kungiyar ta sato, da yin murdiya, da kuma kudaden fansa daga mutane da suka yi garkuwa da su.
Taron na jiya shine karon farko da ministocin harkokin kudi karkashin ministan kudin Amurka Jack Lew, suka zauna a taron kwamitin sulhu.
Kudurin ya bukaci kasashe, su kara kokari na kassara hanyoyin da kungiyar 'yan ta'addan take samun kudade, wacce yanzu take iko da yanki mai fadi a kasashen Syria da Iraqi, yanzu kuma tana fadada zuwa Libya.