A wani kebabben zama baya ga na taron shugabannin duniya na Majalisar Dinkin Duniya da ake yi a New York. Shugaban Rasha Vladamir Putin da Obama na Amurka, sun tattauna su biyu game da ra’ayoyinsu akan kasar Syria.
Inda dukansu ba su yarda da rawar da shugaban Syria Bashar Al’assad ke takawa ba. Amma sun amince da kiyaye hanyar junansu ta fuskar karfin soja.
Wani jami’in fadar Amurka ta White House yace, wannan tattaunawar da shugabannin suka yi ta kusan mintuna 90 a New York, ba tana nufin cimma wata yarjejeniya ba ne, sai dai neman hanyar tattauna matsalar Syria.
Amurka dai bata kallon sojoji da kayan yakin Rasha da ke Syria a matsayin na magance matsalar kasa, illa kurum suna kare kadarorin kasar ta Rasha ne.