A wani jawabi da ya yiwa mutanen Biritaniya game da kasar Siriya Frayim Minista David Cameron ya ce wannan ba batun shiga sharo ba shanu ba ne ko kuma shiga rikice-reikicen kasashen yankin Gabas Ta Tsakiya ba. Wannan kuma in ji shi ba batun sauya matsayin kasar ba ne. Ya ce amma batu ne na yin anfani da makamai masu guba abun da ya keta duk kai'dojin duniya.Ya ce bai kamata duniya ta yi burus da irin wannan katobara ba.
Tuni dai Frayim ministan ya nemi 'yan majalisar dokokin kasar da su dawo daga hutunsu na bazara domin su yi muhawara kan matakan da gwamnatinsa tare da kawayenta Amurka da Faransa zasu dauka. Haka kuma a yau ne Mr. David Cameron yake tattaunawa da kwamitin tsaron kasa da manyan dakarun kasar domin nazarin irin matakan da zasu dauka a kan kasar ta Siriya.
Sai dai kuma wasu 'yan majalisun kasar suna cewa kawo yanzu babu tabbas ko gwamnatin kasar Siriya ke da alhakin kai harin da makamai masu guba ko kuma su 'yan tawayen ne. Sun yi matashiya da kokarin da aka yi na kawar da Saddam Husain lamarin da ya zama wa Amurka da Biritaniya tamkar kashin kifi a makogwaro. Wata 'yar majalisa ta jam'iyyar adawa ta ce da farko dai babu tabbas ko Majalisar Dinkin Duniya zata bada izinin a dauki matakan soji kan gwamnatin Assad na Siriya. Ta kara da cewa abun dariya ne a ce bayan an yi lugudan wuta a kan Siriya washegari Assad yana kan karagar milki inda zai cigaba da cin mutuncin mutanensa.
Muhammed Sani Dauda nada karin bayani.