Domin sanin ko da hakan ta faru abokin aiki Sahabo Imam Aliyu ya zanta da Farfasa Ado Mohammed na Jami'ar Yemen wanda ya yi fashin baki. Ya ce gwamnatin Siriya ta fi 'yantawaye karfi. Idan ba kasashen waje sun taimaka ba to karshenta za'a murkushe 'yan tawayen. Ya yi misali da Libya. Idan ba askarawan Faransa sun shiga ba da ba'a iya kayar da Ghaddafi ba. Anfani da iska mai kurar guba da gwamnatin Siriya ta yi idan lamarin ya tabbata to taba Amurka dama ne ta shiga yakin. Tun can farko Amurka na son shiga to amma bata da hujjar yin hakan. Sai gashi yanzu ta samu dalili.
Amurka da kasashen Turai ba zasu taba yarda ba wata kasa ta mallaki makamai masu guba ko nukiliya sai su kadai domin su dingi anfani da su. Duk wata kasa da shugabanta ya nemi irin wadannan makaman sai sunga bayanshi.
Shigar Amurka cikin rikicin Siriya zai dada dagula alamura a Gabas Ta Tsakiya domin shi Assad yana da makamai da kawaye a duniya da 'yan tsagerar addini wadanda ba zasu bari a murkushesu ba haka a saukake. Farfasa ya ce to amma Amurka na iya cin nasara domin tana fada da 'yan ta'ada gaba daya a duniya don haka idan ta bari aka yi mata kurde a wani wuri to da wuya ta shawo kansu.
Rasha da kasar Sin su ne kawayen Siriya. Idan Amurka ta shiga yakin da farko dangantaka tsakanin kasashen uku zata yi tsamari to amma idan tafiya ta yi nisa zasu shirya domin su ne ke sarafa duniya. Lokacin da bashin Amurka ya yi katutu kasar Sin ce ta sayesu. Don haka kasar Sin ba zata so Amurka ta durkushe ba. Wadannan kasashen duniya uku suna da hanyar da suke daidaita tsakaninsu.
Ga karin bayani.