Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sarauniyar Ingila Ta Kamu Da Covid-19


Sarauniyar Ingila, Queen Elizabeth
Sarauniyar Ingila, Queen Elizabeth

Sarauniyar Ingila Elizabeth, mai shekaru 95, ta kamu da COVID kuma tana fuskantar alamomin marasa tsanani duk da cewa ta karbi allurar rigakafin cutar biyu, amma ana sa ran za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta sama-sama a wannan makon, kamar yadda fadar Buckingham ta fada yau Lahadi.

Fadar ta ce “Sarauniya ta kamu da COVID ne a yau,” Sarauniya na tattare da alamomin sanyi amma ana sa ran za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta sama-sama a Windsor a cikin mako mai zuwa.”

“Za a ci gaba da duba lafiyarta kuma za a bi duk hanyoyin da suka da ce,” a cewar fadar.

Yarima Charles mai jiran gado, dan shekaru 73, a farkon wannan watan ya fice daga wani taro bayan da ya kamu da coronavirus a karo na biyu. Wata majiya daga fadar ta ce ya gana da sarauniyar kwanakin kadan da suka wuce.

A ranar Laraba Sarauniyar ta fadi wa membobin gidan sarauta cewa ba ta iya motsawa sosai yayin da ta aiwatar da aikinta na farko tun lokacin da Charles tare da matarsa Camilla su ka kamu da cutar Covid-19.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG