Gwamnatin jihar Nasarawa tare da hadin gwiwar hukumar tsaro da kare al’umma ta kasa da aka sani da civil defence, ta horar da matasa dubu biyar da dari tara, 5,900 akan yadda za su samo bayanai daga al’umma dan hana afkuwar tashin hankali kafin a auku.
Matasa da aka zabo daga kananan hukumomi goma sha uku na jihar Nasarawa, an horar da su ne kan yadda zasu samar da sahihan bayanai jami’an tsaro dangane da yiyuwar barkewar rikici.
A cikin ayyukan da matasan zasu rika yi sun hada da tabbatar da bin daoka da oda akan tituna, da duba gari masu tsabtace gari, da malaman daji wadanda zasu takaita sare itatuwa dan hana kwararowar hamada.
Kwamandan tsaro da kare al’umma a jihar Nasarawa, Mohammed Gidado Fari, ya bayyana cewa sun haras da matasanne akan samun bayanan tsaro a tsakanin al’umma yadda zasu kare kansu daga hatsari da yadda zsu kula da cincirindon jama’a a lokacin taro tare da matakan da zasu bi wajan kama masu laifi.
Facebook Forum