Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bukatar Ruwa Na Karuwa A Duniya


Yawan jama’a, da kuma canjin da ake samu a yanayin amfani da ruwa na kawo tsaiko akan hanyoyin samun ruwa na duniya, kuma akwai bukatar gwamnatoci su rungumi hanyar samar da ruwa mai tsabta don kiyaye lafiyar al’ummar duniya da kuma cimma bukatun su dake karawa.

Wannan na daya daga cikin sakonnin da aka bayyana a wani sabon bincike da kungiyar raya ilimi da al’adu ta Majalisar Dinkin duniya da ake kira UNESCO ta gabatar a wajen wani taro akan hanyoyin ruwan duniya a kasar Brazil.

Bukatar ruwa na karuwa da kusan kashi daya a duk shekara, duk da cewa sauyin yanayi da gurbatar yanayi, da kuma zaizayar kasa na barazana ga ingancin sa (ruwa) da yawansa a cewar rahoton. In ba yanzu ba, yawancin kasashe sun dogara ne ga hanyoyin ruwa na gargajiya.

Ba sauya hanyoyin samar da ruwa na gargajiya ne burin binciken ba, a cewar UNESCO, amma maimakon haka, don a sami daidaito tsakanin hanyoyin ruwan da dan’adam yayi da kuma a wadanda Allah ya halitta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG