Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Iya Dasawa Mutum Zuciyar Alade


Akwai bukatar koyo ko iya furta wasu kalamai, domin kuwa nan da wasu shekaru kadan, kalamun zasu zama abun amfani ga kowa. A cewar wasu masana kimiyya a jamia’ar Harvard, dake kasar Amurka.

Zurfafa bincike don kara fahimtar yadda ake dashe na wasu gabobin dabbobi zuwa ga jikin dan’adam zai taimaka matuka wajen rage dogaro da akan yi na daukar bangaren jikin wani mutun don dasa shi ga wani, sau da yawa akan yi irin wanan dashe wanda akan cire zuciyar mutun da zummar sakata ga wani.

Sau da dama za’a ga mutane na neman dashe, kodai na huhu, koda, da dai makamantan su, amma babu wanda zai bada kyautar wani bangare na jikin sa da zummar sakama wani.

Bincike ya tabbatar da cewar, wasu kwayoyin hallitar jikin dan’adam, suna kama da na hallitar jikin Alade, domin kuwa har anyi dashen zuciyar Alade ga wani mutun. Haka wasu mutane da suke dauke da cutar da karancin suga a jinin jikin su, anyi musu amfani da bargon Alade.

Haka ma mutane da dama da suke dauke da wasu cututukan da suka shafi fatar jiki, anyi musu amfani da fatar Alade, kuma dukkan su sun samu sauki. Masannan sun kara da cewar, suna kokarin samar da wasu maguguna da zasu kare mutun, daga daukar wasu cututuka daga jikin Alade, idan har an yimishi dashen wani bangare na Aladen.

Suna kuma sa ran nan gaba kadan, za’a iya daukar abubuwa da yawa daga jikin Alade, da zummar dashe ga marasa lafiya kuma su tashi garas, duk dai da cewar dashen kan iya daukar tsawon shekaru biyu kamin yabi jiki.

A bangare daya kuma, wasu daga cikin masana kimiyyar na ganin cewar, akwai bukatar kara fadada binciken, don duk wani abu da ya shefi jikin dan’adam da na dabba sai anyi a hankali, musamman idan ya hada da dashe da suke kira ‘xenotransplantation’ a turance.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG