Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farin Karkanda Daya Tak Da Ya Rage A Duniya Ya Mutu


Masu Kula da gandun dajin Ol Pajeti, a kasar Kenya sun ce karkandan mai shekaru 45 da haihuwa da ake kira Sudan, ya mutu shekaranjiya litinin bayan tsanantar cututtuka masu nasaba da tsufa da yayi fama da su.

Sudan da ya ja hankalin dubban masu yawon bude ido, na daya daga cikin nau'i irinsa da aka yi kokarin a raya a doron duniya da taimakon wasu karkanda mata nau'insa su biyu da suka rage.

A baya an taba ajiye Sudan a gidan ajiye dabbobi na Dver Kralove a janhuriyar Czech, Kafin aka kai shi gandun dajin Ol Pajeta, mai tazarar kilomita Kusan 250 arewa da birnin Nairobi, Inda aka ajiye shi da sauran mata karkanda irinsa su biyu, wadanda ake kira Najin, mai shekaru 27, da Fatu, mai shekaru 17.

Masu kula da gandun dajin sun sha kokarin su hada zuri'a tsakanin dabbobin amma hakar su ba ta cimma ruwa ba. Har sai da suka tallata hoton Sudan a shafin yanar gizo a shekarar da ta gabata, da zummar tara dala miliyan 9 don a iya yada irinsa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG