Kwamishinan lafiya na jihar Dr Tafida Abubakar ne ya bayyana haka a wata hira da manema labarai.
Abubukar ya fadi haka ne a lokacin gabatar da shirin a kauyen korin-makera a karamar hukumar Dutse. Yace za a yi aikin allurar rigakafin na tsawon kwana biyar a kananan hukumomi guda 26.
Kwamishinan yace manufar wannan allurar rigakafin itace, domin ayi wa wadanda basu samu ba lokaci na farko. Yace wannan sake rigakafin zai shafi dukan kauyukan Kirikasamma, Birniwa, Guri, Kaugama da kananan hukumomin Maigatari.
Alhaji Abubakar ya bayyana cewa, duk da haka, baza’a yiwa karamar hukumar Hadeja ba domin bata cikin kananan hukumomin dake cikin hatsarin kamuwa da cutar.
Kwamishinan lafiyan ya kuma kara da cewa, ba a sami wani sabon rahoton bullar curar shan inna a a jihar ba cikin watanni bakwai da suka wuce.
Kwamishina ya yabawa gwamnatin jihar domin kokarinta na kawar da cutar shan inna a jihar.