Shugaban Asibitin Dr Joshua Gyang-Dong wanda ya jagoranci aikin jinyar a Angwan-Waje, kusa da keffi. Ya bayyana cewa, an tsara wannan shiri ne domin taimakon talakawa a kauyukan da ke fama da ciwon ido daban daban. Ya kuma yi kira ga sauran masu aikin lafiya da su hada hannu da su, domin shawo kan kalubalen lafiya da mutane ke fuskanta, musamman talakawa da mazauna kauyuka.
Shima shugaban sashen ido na asibitin. Tunde Owoyele, ya bayyana cewa, wannan shirin zai taimaki masu fama da ciwon ido. Bisa ga cewarshi, shirin zai rage yawan cutar idanuwa a al’umma, kuma ya kuma bayyana cewa za’a yi gwajin idanu kyauta.
Shugaban Asibitin yace, bayan yiwa masu ziwon ido aiki, za a ba wadanda ke bukatar magani da gilasai kyauta idan suna bukata domin su iya gani sosai.