Professa Idoko yayi wannan kira ne a wajen wani taron kwana daya da aka yi da nufin neman sababbin matakan yaki da kwayar cutar HIV a matsayin mataki na gaba da ya biyo bayan taron da shugaban kasa Goodluck Jonathan ya halarta kan yaki da cutar kanjamau da ake kira PERP a watan Mayu shekara ta dubu biyu da goma sha biyu.
PERP wani shiri ne da aka kaddamar da nufin yaki da matsalar cutar kanjamau a nahiyar Afrika.
A cikin jawabinshi wajen taron, shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana cewa, koda yake Nigeriya tana kokari sosai wajen yaki da cutar kanjamau, duk da haka akwai sauran aikin da ya kamata ayi zuwa 2015. Yace ana bukatar sabon salo a fannin matakan kariya da kuma magungunan jinya, abinda ba zai yiwu ba sai da kudi.
A cikin wannan shekata ta 2013 aka cika shekaru 32 da bullar kwayar na cutar HIV a duniya, kuma a halin yanzu cutar tafi yawa a kasashen nahiyar Afrika dake yankin hamada.