Masanan lafiya guda uku, Dr. John Egbuta, Dr. Bisola Animashaun, da Dr. Alfred Dion sune suka bada wannan shawara a wata ganawa da ‘yan jarida a lagos.
Dr. Egbuta, ma’aikaciyar sashin abinci da kungiyar UNICEF a lagos, tace yara ne suka fi samun ribar shan mama, kuma babu wata matsala ko illa mace ta ba jaririn da ba nata ba nononta idan bukata ta tashi muddar ba a riga an yaye jaririn ba.
A cikin bayanin ta, Dr. Egbuta tace, tilas ne a yiwa macen da zata shayar da dan da ba nata ba gwajin cutar cida sosai, domin wannan ce cutar da zata iya zama da cutarwa a maimakon gyara ga jaririn idan ya kasance macen da ta bashi nonon tana dauke da cutar kanjamau ba tare da an sani ba.
Ta kuma kara cewa, madarar nono, madara ce. Tana da amfani kwarai da gaske ga yaro, saboda wani lokaci idan uwar ta rasa ranta wajen haihuwa, ana iya sa kakar yaron ta bashi mama.”