“Zai shafi ayyukan yau da kullum, kaima ka sani, don ance yanzu baza ayi amfani da kudi wajen kyautata rayuwar talakawa, sai dai harkar tsaro.” A cewar Ahmed Sirajo. “Domin haka muna gani kamar akwai wata manufa a wannan lamari”.
Da yake tsokaci akan matakan da jihohi zasu dauka biyo bayan rike kudadensu, Mr. Sirajo yace:
“Ya kama ala tilas a garzaya Kotu, saboda wannan kalubale ne ga demokradiyya ita kanta. Ba ma ga mu a jihar Adamawa ba, saboda wannan doka bata da hurumu, bata da hujja a tsarin mulkin Najeriya. Babu inda aka ce Shugaban kasa, in ya saka dokar ta baci, ya cire gwamna, ko ya kwace ikon da gwamna yake da shi.”
Ran 14 ga watan nan na Mayu ne Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ya kaddamar da dokar ta baci a jihohi uku dake arewa maso gabashin Najeriya, inda dakarun Najeriya suka isa domin kwato wasu sassan jihohin da kungiyar Jama’atu Ahlil Sunnah Lil Da’awati Wal Jihad da ake kira Boko Haram, suka kame.
Tun bayan kaddamar da dokar ta bacin ne, aka kafa dokar hana yawo a wasu yankunan jihohin, sannan a katse layukan wayoyi abun da yasa mutane da yawa a cikin damuwa da zaman zulumi. An sassauta dokar hana yawo a wasu jihohin, amma rahotanni na nuna cewa har yanzu layukan wayoyin tarho a rufe suke.