‘Yan wasan Flamingos sun sauka a Abuja, babban birnin Najeriya bayan da suka lashe kyautar tagulla a gasar cin kofin duniya ta mata ‘yan kasa da shekara 17 da aka yi a India.
Najeriya ta doke Jamus a bugun fenariti bayan da aka tashi 3-3 a wasan neman gurbi na uku a gasar.
Tawagar ‘yan wasan ta sauka a filin tashin jirage na Nnamdi Azikwe a ranar Talata inda jami’an hukumar kwallon kafar Najeriya ta NFF suka tarbe su.
Jim kadan bayan saukarsu, ministan wasanni da matasa, Sunday Dare, ya gana da ‘yan wasan inda ya ba su tabbacin cewa gwamnati za ta taimaka musu ta yadda za a karfafa tawagar.
Rahotanni sun yi nuni da cewa Kyaftin din Super Eagles Ahmed Musa, ya bai wa tawagar ‘yan wasan kyautar miliyan uku kuma nan take da suka sauka aka ba su cek din kudin.