Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jawabin Shugaban Amurka Joe Biden Kan Halin Da Kasar Ke Ciki


Joe Biden
Joe Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya fada a jiya Talata cewa, labarin Amurka labari ne na ci gaba da jajircewa, yayin da yake jawabi a kan halin da kasa ke ciki da ya maida hankali a kan manufofin tattalin arzikin na cikin gida, inda ya kara da kira ga ‘yan adawa na Republican da su hadu su yi aiki tare.  

Shugaba Biden ya fadawa 'yan majalisan cewa, “Shekaru biyu da suka shude, cutar COVID ta rufe mana kasuwanni, ta rufe makarantun mu kana ta yi mana illa da yawa,”

Ya ce “A Yau COVID bata da tasiri a kan rayuwar mu.”

“Shekaru biyu a baya, dimokaradiyyar mu ta fauskanci gagarumar barazana tun bayan yakin basasa. Amma a yau, ko da yake tana da dan matsaloli, dimokaradiyyar mu na nan da karfinta.

Yayin da yake fuskantar ‘yan Republican da ke da rinjayi a majalisar wakilai, Biden ya ambato wasu dokoki da suka samu amincewar ‘yan majalisar Republican da Democrat da suka hada da gagarumin kudurin gine-gine, da taimakon Ukraine da kuma kudurin kare ‘yancin auren jinsi daya.

“Ga abokai na ‘yan Republican, idan zamu yi aiki tare a majalisa da ta gabata, babu wata hujjar da zata hana mu aiki tare kuma mu samu matsaya a wannan sabuwar majalisar,” inji Biden

Biden ya ce don ci gaba da samun karfin tattalin arziki a duniya, Amurka na bukatar ingantattun ababen more rayuwa, kuma ya ce sabbin ka'idoji za su bukaci ayyukan samar da ababen more rayuwa na tarayya su yi amfani da kayan gini da aka yi a Amurka kadai.

Kama daga "itatuwa, gilashi, kayan hada bango, layin sadarwa," in ji shi. "Kuma ya ce a karkashin jagorancina, hanyoyin Amurka, gadojin Amurka da manyan hanyoyin Amurka su ma za a yi su da kayayyakin Amurka ne."

Ga baki daya, shirin tattalin arzikinsa ya maida hankali ne a kan zuba jari a wurare da cikin mutane da aka manta da yin hakan.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG