Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jawabin Shugaba Biden Ga Shugabannin Kasashen Afirka


Shugaban Amurka Joe Biden, lokacin da yake jawabi a taron kolin shugabannin Amurka da Afirka.
Shugaban Amurka Joe Biden, lokacin da yake jawabi a taron kolin shugabannin Amurka da Afirka.

Shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar da jawabinsa ga shugabannin Afirka da suka hallara a birnin Washington, cewa Amurka za ta iya zama babbar hanyar bunkasa nahiyarsu a shekaru masu zuwa.

Shugaba Biden ya sanar da sabbin tsare-tsare na kasuwanci da saka hannun jari a Afirka, yayin da yake jawabi a taron kolin da gwamnatinsa ta shirya a birnin Washington DC, wanda ya samu shugabanni daga sassan nahiyar.

Biden ya yi alkawarin karfafa hadin gwiwa, yana mai cewa ba za a iya magance kalubalen duniya ba "ba tare da shugabancin Afirka a kan tebur ba." Taron dai shi ne irinsa na farko tun shekarar 2014.

Nan gaba kadan a yau Laraba, Biden zai halarci wata liyafar cin abinci da shugabannin Afirka a fadar White House.

Gwamnatin Biden ta na sanya Amurka a matsayin amintacciyar abokiyar zama mai inganci, don taimakawa wajen habaka zabe na gaskiya da dimokaradiyya da kiwon lafiya.

Sai dai wannan yunkurin na zuwa ne a daidai lokacin da China ta yi wa Amurka nisa, a fannin zuba jari, a yankin kudu da hamadar sahara, wadda ta zama fagen yaki a fafatawa tsakanin manyan Kasashen duniya.

Shugaba Biden
Shugaba Biden

Fadar White House ta ce taron ya fi zama zaman saurare tare da shugabannin Afirka fiye da kokarin dakile tasirin Beijing, amma manufofin Biden ya mamaye komai: Amurka na cikin yakin neman zabe don tabbatar da dimokiradiyya na iya fitar da mulkin kai.

Wannan sakon ya fito karara a cikin al'amuran ranar Laraba: jawabin Biden a gaban shugabannin 'yan kasuwa daga nahiyoyi biyu, karamin zama na shugaban kasa tare da wasu shugabannin nahiyar wadanda kasashensu za su gudanar da zabe a shekarar 2023, da kuma wata liyafar cin abinci da uwargidan shugaban kasa ta shirya wa dukkan shugabannin da matansu a fadar White House.

Shugaban Amurka Joe Biden
Shugaban Amurka Joe Biden

Wannan wani bangare ne na wani sabon yunkuri na bunkasa alaka da nahiyar da ke fuskantar kalubalen muradun Amurka, saboda burin kasar China na tsaro da cinikayya da zuba jari da ba da lamuni. Sabanin haka, birnin Beijing na gudanar da nasa manyan tarurruka da Afirka a duk bayan shekaru uku fiye da shekaru ashirin.

Yayin da gasar tsakanin China da Amurka ta kasance a baya, jami'an Amurka sun yi watsi da tsara taron a matsayin yakin neman tasiri. Washington ta yi watsi da sukar da ta ke sha, kan ayyukan ba da lamuni da ayyukan more rayuwa na Beijing a daidai lokacin da wasu shugabannin Afirka suka yi kira ga karin shugabancin Amurka.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG