Shugaba Obama ya ce, idan har makamin nukiliya guda daya ya fashe, ta yiwu a birnin New York ne, ko a Moscow, ko Islamabad, ko Mumbai, ko Tokyo, ko Tel Aviv, ko Paris ko Praha- zai iya kashe dubban jama’. Kuma ko ina ne abun ya faru, babu karshen illar da za a iya fuskanta a duniya ta fuskar tsaro, kariya, tattalin arziki, al’umma, da rayuwarmu dungurungum.
Daga wannan jawabi na shugaba Obama, an gudanar da tarurrukan koli na tabbatar da tsaron nukiliya a shekarun 2010 da 2012 da kuma 2014, wanda ya ingiza kasashe da dama wajen bunkasa tsaron nukuliyarsu don hana su fadawa hannun ‘yan ta’adda. Amma duk da wadannan nasarorin, har yanzu akwai aiki wurjanjan game da muhimmancin gurorin da wadannna tarurrukan basu cimma ba.
Shugaba Obama ya fada a wani jawabi da yayi a shekarar 2009 cewa, kasancewar makamin nukuliya a hannun dan ta’adda wata babbar barazana ce gatsaron duniya.
A yau alhamis, aka bude taron koli na hudu na tsaron nukiliya a nan Washington, inda shugabanni fciye da 50 ciki har da shugaba Buhari na Najeriya suke halarta.