Jamus ta lashe kofin Gasar Duniya ta ‘yan kasa da shekaru 17 da aka yi a Indonesia bayan doke Faransa.
‘Yan wasan na Jamus sun lashe kofin ne da bugun fenariti inda aka tashi da ci 4-3 a karawar da suka yi da Faransa.
An shiga zangon bugun na fenariti ne bayan da aka tashi kunnen doki da ci 2-2
Jamus ta buga mintina 21 na karshe da ‘yan wasa 10 bayan da aka ba Osawe katin gargadi a karo na biyu.
Jamus ce ta fara zura kwallon farko ta hannun Paris Brunner wanda ya ci da fenariti.
Wannan shi ne karon farko da Jamus ta kai zagayen wasan karshe a wannan gasa tun bayan 1985.
Dandalin Mu Tattauna