Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta sanya ranar Talata a matsayin wa'adin da za a bayyana sha'awar karbar bakuncin gasar a hukumance, sai dai matakin da Australia ta dauka na janyewar ya bari Saudiyya ta kasance 'yar takara daya tilo da aka ayyana - abin da ya bata wa 'yan rajin kare hakkin bil'adama da dama rai.
"Mun bincika damar mu ta karbar bakuncin gasar cin kofin duniya ta FIFA, kuma bayan yin la'akari da dukkan abubuwa - mun kai ga ƙarshe ba za mu amshi balkwancin gasar 2034 ba," in ji hukumar kwallon kafa ta Australia a cikin wata sanarwa.
Yanzu FIFA za ta ba Saudiyya amincewar wucin gadi a matsayin mai karbar bakwancin gasar- shawarar da mai yuwuwa za ta yanke a shekara mai zuwa - amma yanzu ana kallon lamarin tamkar shiri ne kawai. Wannan zai kawo karshen yunkurin da Saudiyya ke yi na cimma burinta ta zama jigo a fagen wasanni a duniya, inda tuni ta kashe makudan kudade wajen kawo dimbin ‘yan wasan kwallon kafa a gasar cikin gida, da sayen kulob din Newcastle na Ingila, da kaddamar da yawon shakatawa na gasar kwallon LIV Golf da kuma wasannin damben boxing.
Sai dai kuma da alama FIFA na son share fagen don Saudiyya ta samu daman daukar nauyin gaggarumin wasanta, lamarin da ya janyo suka daga masu fafutuka wadanda suka ce hukumar ta fallasa kanta game da irin alkawurran da ta dauka na kare hakkin dan Adam a matsayin wani yaudara.
An bayyana shirin kashe kudaden wasanni na Saudiyya da yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ya amince da shi a matsayin amfani da wasanni wurin wanke kansa da kuma tausasa kimar kasar da ake dangantawa da mai tarihin rashin mutunta hakkin mata da kuma kisan dan jaridar nan Jamal Khashoggi a shekarar 2018.
Shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino ya kulla wata alaka ta radin kansa da hukumar kwallon kafa ta Saudi Arabia da ma Yariman mai jiran gado, kuma tuni ake ganin yana kokarin karkatar da akalar harkokin kwallon kafa ta duniya zuwa daular.
Kasar Qatar dai itace ta dauki bakwancin gasar ta baya da aka yi a watannin Nuwamba-Disamba, a tsakiyar kakar wasannin Turai domin kaucewa tsananin zafi na lokacin rani kana da alama za a tura gasar da ake sa ran yi a Saudiyya daga watannin Yuni-Yuli da aka saba wasan.
Da farko dai kungiyar kwallon kafa ta Indonesia ta nuna sha’awarta na neman hadin gwiwa da wasu kasashe baicin Australia, wanda ake ganin kasashen za su hada da Malaysia da Singapore, amma hakan ya dusashe lokacin da Indonesia ta goyi bayan Saudiyya.
Dandalin Mu Tattauna