Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

SUDAN TA KUDU: Gwamnati Ta Sallami Shugaban Babban Bakin Kasar Da Mataimakinsa


 Salva Kiir, Shugaban Sudan ta Kudu
Salva Kiir, Shugaban Sudan ta Kudu

A wani yunkuri dake da nasaba da tattalin arziki, shugaban kasar Sudan ta Kudu Siva Kiir ya sallami shugaban babban bankin kasar tare da mataimakinsa

Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir ya sallami gwamnan babban bankin kasar shi da mataimakinsa na farko ba tare da bada wani bayani ba.

A daren laraba ne shugaba Kiir ya bada wata sanarwar dokar data cire Gwamnan na babban bankin kasar Othom Rago Ajak shi da mataimakin sa Dier Tong Ngor daga mukaman su.

Sai dai wani masanin tattalin arzikin kasar ya ce sauke wadan nan mutanen daga makamansu ba zai rasa nasaba da rashin hobbasarsu ba ne wajen ganin sun farfado da tattalin arzikin kasar dake durkushewa.

Wata majiya mai tushe daga babban bankin kasar ta tabbatar wa wani shirin da ake gabatarwa a wannan gidan Radiyon da ake kira South Sudan In Focus cewa ba shakka an samu canjin shugabancin wannan bankin.

Sai dai sakataren yada labaran shugaba Kiir Ateny Wek Ateny bai bada cikakken tabbacin wannan canjin ba.

Yace bai ga wannan dokar ba tukuna , “a saboda haka ba zanyi sharhi akan jita-jita ba”. Yaci gaba da cewa idan har akwai wata dokar da shugaba ya fitar, game da sauke gwamnan babban bankin kasa, to wuri na farko da za a fara jin wannan labarin shi ne gidan Radiyon tarayya na kasar.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG