'Yan tawaye a Sudan ta kudu sun yi watsi da yarjejeniyar zaman lafiya da gwamnatin kasar tayi ikirarin cewa duka sassan biyu sun amince dashi. Wannan labarin ya kashe gwuiwar dokin da ake dashi na ganin an kawo karshen yakin basasar kasar na kusan shekaru biyar.
A rahoton da Mohammed Yusuf ya aikowa Muryar Amurka daga Nairobi, ya ce a cikin wata sanarwa da kungiyar 'yan tawayen Sudan da Kudu da ake kira SPLM ta ce hakika an tattauna kan batun daunin iko- amma ba'a cimma matsaya a hukumance akai ba.
Tunda farko wata hadakar 'yan hamayyar kasar data kunshi jam'iyu tara,wacce ake kira South Sudan Opposition Alliance da turanci ta yi watsi da yarjerjeniyar.
Kwaje Lasu, shi ne kakakin hadakar, ya ce
Bamu da hanu a cikin yarjejeniyar. Wannan ya kaucewa amannar da mukayi da damawa da kowa. Bugu da kari, duk shawarwarin da aka yi da sunan daftari kan daunin iko-hakan bai tabo baki daya musabbabin rikicin ba."
Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir, da shugaban 'yan tawaye Riek Machar sun gudanar da shawarwari ranar Asabar a birnin Entebbe, wani ziri a tafkin Victoria.
Duk da cewa ba'a tsammain a cimma matsaya da zata warware fitinar baki daya, akwai tsammanin a sami zaman lafiya ganin matakai da aka dauka na baya bayan nan.
Sassan biyu da suke gaba da juna, sun amince ranar Jumma'a su janye dakaru daga birane, bayan da aka cimma yarjejeniyar zaman lafiya a karshen watan Yuni.
Facebook Forum