Wani mai Magana da yawun babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ya musanta zargin da ake yi na cewa jam’iyyar ta yi watsi da Sakataren watsa labaranta Oliseh Metu, a yakin da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ke yi da cin hanci da rashawa.
Ana dai zarginsa ne da karbar naira miliyan dari hudu daga tsohon mai baiwa shugaba shawara kan harkar tsaro, Sambo Dasuki, inda ya kuma ajiye kudaden a asusun sa.
Rahotanni sun ce ainihin kudin an ware su ne domin sayen makaman da za a yaki kungiyar Boko Haram, amma Metuh ya yi ikrarin cewa an bashi kudin ne domin yin wasu ayyukan jam’iyyar PDP a lokacin tana mulki.
Sai dai mataimakin kakakin jam’iyyar ta PDP na kasa, Abdullahi Jalo, ya ce jam’iyyar ba za ta dauki alhakin karbar kudin ba, domin an saka ne a wani asusu na daban ba na jam’iyyar ba.