Duk dankwangilar da bai kammala aikin da aka ba shi ya yi a tashar jirgin sama ba to ya kuka da kansa domin gwamnati zata dauki matakin da ya dace. Stella Oduah ministar harkokin jiragen sama ta yi wannan gargadin lokacin da take yin rangadin tashoshin da ake gyarawa. Ministar ta ce duk wanda yake aiki a kowace tasha babu wanda ba'a baiwa isasshen kudi ba domin haka babu wani hujjar bata lokaci.
Tawagar ta ziyarci tashoshi guda bakwai inda ake aiki. Koina kuma aikin ya kankama sai dai matakin aikin ya sha banban. Misali a Yola an gama aikin kwaskwarima amma kayan da aka yi anfani da su ba ingantattu ba ne. Wani ma'aikaci a tashar ya ce kayan da aka yi anfani da su ba masu inganci ba ne.
A filin jirgin sama na Sokoto aikin tubarkalla. Wani da aka fara aikin a gabansa ya ce aikin da aka yi ya yi kyau domin duk wanda ya san tashar da yanzu idan ya ganta zai yi mamaki. A Ilorin ma ginin da aka sabunta shi ma tubarlkalla.A Calabar ma ana aiki gadan gadan duk da an kammala wani bangaren. Wata fasinja da ta saba yin anfani da tashar ta yaba da aikin.
Tashar Enugu ita ce ta karshe a ziyarar nan ma aiki ya cigaba. Shugaban kungiyar Kirista reshen jihar Enugu ya yabawa ministar da kokarin da take yi.