Wadannan mutanen tara sun amince su shiga gwamnati mai ci yanzu lamarin da ya jawo masu fushin uwar jam'iyyar tasu. Malam Tambura Yusuf yace sun bi ka'idodin jam'iyyarsu da na kasa su ne dalilin da sukasu yin nasara a kotu inda aka tabbatar da korar da suka yiwa mutane taran. Wato shari'ar ta nuna su mutanen tara ke kan hanyar karya.
A cikin shirin dimokradiya ba zaka iya kana cikin jam'iyyar adawa ba kana kuma ka ce kana cikin jam'iyya mai mulki. Hakan nan ba dimokradiya ba ne.Idan mutum na so sai ya bar jam'iyyar adawa ya shiga wadda take mulki.
Lauyan dake kare wadanda aka kora yace korar bata zauna ba tukunna domin ta wucin gadi ce. Yanzu suna hada takardun daukaka kara zuwa kotu ta gaba.Lauyan ya hakikance kotun ma bai karbi kararsu ba.
Dama can baya ita jam'iyyar MNSD tace ba zata amince da wasu daga cikin 'ya'yanta su shiga gwamnatin hadin gambiza ba da shugaba Yusuf Mamman ya yi yunkurin kafawa a shekarar 2013. Shiga cikin gwamnati da mutanen tara suka yi ya taka dokar da jam'iyyar ta shimfida tun farko.