Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya ta cafke wata matashiya Bolatito Solabi, mai shekaru 34 da haihuwa a filin sauka da tashin jirage na kasa da kasa da ke birnin tarayya Abuja dauke da miyagun kwayoyi masu tarin yawa.
An kama matashiyar ne tare da wani mai suna Victor Chukwu, wanda aka damke kayan mayen nau’in Heroin da nauyin su ya kai gram 865.
Mujallar Daly Post ta wallafa cewa, an sami labarin cewa Solabi, wadda ta kammala karatu a makarantar kimiyya da fasaha ta jihar Ogun ta shiga jirginne daga kasar Habasha, yayin da jami’an suka gano miyagun kwayoyin a cikin jakunkunan ya guda biyu.
Da yake jawabi akan lamarin, shugaban hukumar Lawan Hamisu ya bayyanawa mujallar Punch, cewa kamen ya nuna cewa da alamu yankin kudanci da gabashin Nahiyar Afrika sun fara shi’awar harka da kungiyoyin fasakwaurin miyagun kwayoyi na yankin kudancin nahiyar da ‘yan kasar Malawi da Kenya da kuma Tanzaniya, inda suke bi domin fataucin miyagun kwayoyin daga Pakistan zuwa Najeriya, kuma yawancin su sun fi shiga wannan jirgi.
Mai Magana da yawun hukumar ya bayyana cewa an kama miyagun kwayoyi da nauyin su yaka kilogiram 26, cikin watanni uku da suka gabata.
Facebook Forum