Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Leken Asirin Afghanistan Sun Tabbatar da Mutuwar Shugaban Taliban


Shugaban Taliban Mullah Akhtar Mansoor,
Shugaban Taliban Mullah Akhtar Mansoor,

Kungiyar leken asirin kasar Afghanistan ta tabbatar cewa harin da Amurka ta kai da jiragen saman yaki a kasar Pakistan kusa da kan iyakar kasar da Afghanistan ya kashe shugaban Taliban Mullah Akhtar Mansour

Kasar Pakistan tace Amurka tayi mata bayani bayan ta kai harin da jiragen saman yakin dake tuka kansu da kansu.

A saboda haka ta caccaki Amurka domin a cewarta Amurkan ta keta ka'idar diyaucinta. Haka kuma Pakistan ta ki ta tabbatar da kashe shugaban Taliban din.

Jiya Lahadi sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya fada a ziyarar da yake yi a kasar Myanmar cewa an auna Mullah Akhtar Mansour saboda yana jawowa amurkawa da 'yan Afghanistan da kuma jami'an tsaron Afghanistan barazana kuma baya goyon shawarwarin samun zaman lafiya.

Wasu jami'an Taliban sun tabbatar da mutuwar shugaban nasu kodayake suna dari darin bayyana sunayensu. Sun ce majalisar zartaswar kungiyar ce zata bada sanarwar karshe akan lamarin

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG