Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Pakistan Ta Sha Alwashin Yaki Da Ayyukan Ta’addancin A Kasar


Wannan hari na baya-bayan nan ba zai dakarun kasar su razana ba.

Firai ministan Pakistan, Nawaz Shariff, ya sha alwashin daukan mataka yaki da ayyukan ta’addancin a kasar bayan harin da aka kai a jiya Lahadi da ya kashe mutane 72, ciki harda kananan yara.

Ya ce ya san maharan suna kai harin ne a wuraren da jama’a suke saboda, dakarun kasar sun takura su, yana mai jaddada cewa wannan hari na baya-bayan nan ba zai sa su razana ba.

Wani kakakin soji a yau Litinin ya ce jami’an tsaron gudanar da samame, kuma an cafke mutane da dama da ake zargi na da hanu wajen hsirya hare-haren.

Tuni dai reshen kungiyar Taliban da ya balle daga uwar kungiyar wanda ake kira Jama’atul Ahrar ya dauki alhakin wannan hari wanda aka kai akan kiristoci marasa rinjaye a wajen wani shakatawa da ke Lahore.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG