Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Taliban ta Halaka Sojojin Amurka Shida a Afghanistan


Ashton Carter, Sakataren Tsaron Amurka
Ashton Carter, Sakataren Tsaron Amurka

Ma'aikatar tsaron Amurka ta tabbatar da mutuwar sojojinta shida, sakamakon wani harin kunar bakin wake da aka kai jiya Litinin kan sojojin kungiyar tsaro ta NATO, wadanda suke sintiri kusa da sansanin mayakan sama dake Bagram a Afghanistan.

Kungyar Taliban ta dauki alhakin kai harin, tana mai ikirarin cewa wani dan kunar bakin wake kan babur ne ya kai harin ya kashe sojoji 19. Kungiyar NATO tace zata binciki harin.

Sakataren tsaron Amurka Ashton Carter, yace harin, yana tunatarwa kan irin hadarin da sojojin Amurka suke fuskanta a kowace rana a Afghanistan.

Carter yace, harin ya kuma jikkata wasu sojojin Amurka biyu, da kuma wani ma'aiakci wanda dan kwangila ne.

Fadar White House ta shugaban Amurka ta aike da ta'aziyya ga iyalan sojojin da harin ya rutsa da su, ta kara da cewa ba zata yi kasa a guiwa ba wajen daukan mataki kan barazana r ta'addanci da ya addabi yankin.

Majalisar Dinkin Duniya tana nanata kiran da take yiwa kungiyar Taliban ta gudanar da shawarwari da gwamnatin Afghanistan.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG