Mambobnin kasashen kungiyar tarayyar turai ta EU sun koma zaman tattaunawar da suke yi a kokarinsu na samar da kudaden tallafin da za su taimakawa yankin a yakin da ake yi da cutar coronavirus.
Tattaunawar ta su na da nasaba da kasafin kudi dala tiriliyan 2 da ake so a samar don da yaki da annobar.
Da tsakar ranar yau ake sa ran ci gaba da tattaunawar, wacce asali ya kamata a kammala ta a ranar Asabar.
Firayim Ministan Holland, Mark Rutte ya ce shugabannin na samun ci gaba a tattaunawar, sannan shugaban gwamnatin Austria Sebastian Kurz ya ce duk da cewa tattaunawar ta yi tsauri, “za mu kasance masu gamsuwa da sakamakon da zai bayyana a yau.”
A kwanakin da aka kwashe a wannan taro, an ga yadda kasashe mafiya karfin tattalin arziki da ke arewacin nahiyar turai, wato Austria, Denmark, Findland, Holland da kuma Sweden, suke sa-in-sa da takwarorinsu na kudanci, wadanda suka fi fuskantar matsalar ta coronavirus – suke kuma samun goyon bayan Jamus da Faransa.
Su dai kasashen na arewaci, suna so a saka matakan tsuke bakin aljihu a yarjejeniyar da za a kulla yayin da su kuma sauran kasashe irinsu Italiya da Spain suke so a sassauta matakan.
Facebook Forum