Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ce Da Laifin Rugujewar Tattaunarwarmu - China

Mataimakin ministan ma'aikatar kasuwancin China, Wang Shouwen
Mataimakin ministan ma'aikatar kasuwancin China, Wang Shouwen

Matakin fidda sunayen, martani ne ga matsayar da Amurka ta dauka, na haramta siyar da wasu kayayyakin da ake hadawa a Amurkan ga kamfanin sadarwa na Huawei da wasu abokanan huldarsa 68.

China ta ce, hukumomin Washington ne ke da alhakin rugujewar tattaunawar da ake yi domin neman shawo kan takaddamar cinikayyar da ke faruwa a tsakanin kasashen biyu, tana mai cewa ba za ta mika wuya bori ya hau ba.

A wani mataki na dora laifin akan Amurka, China ta fitar da wata sanarwa a yau Lahadi, inda ta ce Amurka ce ta ja baya a tattaunawar da ake yi kan batun karin kudaden haraji, matakin da ta ce ba zai samar da masalaha ba.

Tun dai da tattaunawar ta ruguje a farkon watan nan, hukumomin Beijing suka kara mayar da hankali wajen daukan matakai na martani, dangane da karin kudaden haraji zuwa kashi 25 da Amurkan ta yi akan kayayyakin China da kudinsu ya kai dala biliyan 200.

Ita ma Chinan ta yi ta yada farfaganda a kafafen yada labaranta, inda a ranar Juma’ar da ta gabata, ma’aikatar harkokin kasuwancin kasar, ta fitar da jerin sunayen wasu kamfanoni da ta ce ba ta amince da su ba.

Matakin fidda sunayen, martani ne ga matsayar da Amurka ta dauka, na haramta siyar da wasu kayayyakin da ake hadawa a Amurkan ga kamfanin sadarwa na Huawei da wasu abokanan huldarsa 68.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG