FILATO, NAJERIYA: A wata sanarwa mai dauke da sa hannun daraktan yada labarai da hulda da jama’a a ofishin gwamnan Jihar Filato, Makut Simon Macham, Lalong ya nuna damuwarsa kan yawaitan hare-hare da lalata gonaki, satar dabbobi da sauran kadarori a yankin na karamar hukumar Bokkos.
Sanarwar ta ce gwamnati ba za ta zuba ido tana kallon ‘yan ta’adda suna kisan mutane ba gaira ba dalili ba, don haka ya umurci jami’an tsaro da su gaggauta bankado wadannan maharan.
Kansila mai wakiltar Butura, Isaac Julson ya ce, tun ranar Litinin ne aka yi arangama da ‘yan bindigan, daga bisani suka zo suka hallaka mutane goma sha daya.
Shi ma mai unguwar Kuba, Mabas Kuba ya ce suna bukatar gwamnati ta turo musu jami’an tsaro da tsare lafiyarsu da dukiyoyinsu.
A gefe guda kuwa, Alhaji Hassan Mongyaldi, mataimakin shugaban kwamitin sasanta tsakanin makiyaya da manoma da sarkin Butura ya kafa, ya ce ya samu labarin kisan wasu Fulani biyu a yankin da lamarin ya faru, don haka suke fadakar da jama’a a kan muhimmancin zaman lafiya.
Tuni dai kwamandan rundunar Special Task Force, Manjo Janar Ibrahim Ali ta kai ziyarar gani da ido a yankin, inda ya umurci jama’an tsaro da su kamo wadanda suka aikata kisan, don su fuskanci hukunci.
Kwamandan ya kuma bukaci jama’a da su kaucewa daukan doka a hannunsu.
Saurari cikakken rahoto daga Zainab Babaji: