Hakan na kunshe ne a cikin sakon da SERAP ta wallafa a shafinta na X a yau Litinin, inda ta bayyana cewar jami’an Dss sun mamaye harabar ofishinta harma sun bukaci kaiwa ga daraktocinta.
SERAP ta bukaci Shugaban Kasa Bola Tinubu ya gaggauta sanya baki a lamarin tare da umartar hukumar tsaro ta DSS ta dakatar da abinda ta bayyana da harin babu gaira babu dalili akan hakkokinta dana ‘yan Najeriya.
An ruwaito sakon Na X na cewa, “a yanzu haka jami’an hukumar tsaro ta DSS na mamaye da ofishinmu na abuja ba bisa ka’ida ba, inda suka bukaci ganin daraktocinmu.
“Wajbi ne Shugaba Tinubu ya gaggauta umartar hukumar tsaro ta DSS ta kawo karshen wannan cin zarafi da razanarwa da kuma kai hari kan hakkokin ‘yan Najeriya.”
Dandalin Mu Tattauna