Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Cafke Fursunoni 10 Cikin Fiye Da 100 Da Suka Fice Daga Gidan Yarin Suleja


Jami'an Hukumar Kula da Gidan Yarin
Jami'an Hukumar Kula da Gidan Yarin

Jami’an hukumar na farautar fursunonin da suka tsere  kuma kawo yanzu sun samu nasarar cafke 10 daga cikinsu tare da taimakon wasu jami’an tsaro.

WASHINGTON DC - Akalla fursunoni 118 ne suka tsere daga gidan yari bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya a daren jiya Laraba, ya lalata ginin da ke Suleja kusa da babban birnin tarayyar Najeriya, kamar yadda kakakin hukumar kula da gidan yarin ta bayyana.

An dauki tsawon sa'o'i da dama ana ruwan saman kamar da bakin kwarya, inda yayi sanadiyyar rushe wasu sassan gidan yarin da suka hada da katanga da gine-ginen da ke kewaye, kamar yadda kakakin gidan yarin Adamu Duza ya sanar a yau Alhamis.

Duza ya ce "Muna aiki tukuru don ganin mun kamo sauran."

Yace “An kuma umurci jama’a da su sanya ido sosai tare da kai rahoton ga hukumar tsaro mafi kusa”

Tserewa daga gidajen yari ya zama babbar matsalar tsaro a Najeriya da cunkoson jama'a, da karancin kudade, da kuma matakan rashin tsaro suka haifar.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG