Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jama'ar Kasar Sudan Ta Kudu Na Ci Gaba Da Arcewa Sansanin 'Yan Gudun Hijira


Rahotanni na cewa motocin bas-bas shake da ‘yan gudun hijirar kasar Sudan ta Kudu daga bakin iyakar arewacin Uganda, na zuwa sansanin ‘yan gudun hijira wanda yake nan ne sabon martattararsu, saboda rashin sanin abinda ka iya biyo baya

Yanzu dai wannan sansanin shine sansanin ‘yan gudun hijira mafi girma a Africa, wanda sai kara girma yake yi kullun. Daya daga cikin bakin iyakokin da kuma ake tsallakowa zuwa wannan sansanin shine na Busia, wanda da kafa ma ana iya takowa daga Sudan ta Kudu zuwa kasar Uganda.

Sai dai kuma sojoji ‘yan tawaye sun sa ido ga bangaren masu shigowa cikin kasar ta Uganda, yayin da jami’an tsaron kassar Uganda, suna daya gefen suna tantance masu shigowa kasar tasu, suna binciken ganin basu shigo da makamai ba.

Haka kuma kasuwa ta bude wa masu babur domin ko suna daukar mutane suna tsallakawa dasu ana biyan su, Amma kuma galibin ‘yan gudun hijiran suna shiga cikin wannan sansanin ne hurjanjan, domin ko suna fama da yunwa, kishin ruwa da gajiya.

Daya daga cikin wadannan ‘yan gudun hijiran wani dan shekaru 30, mai suna Abui Tadeo wanda kafin ya samu kansa cikin wannan yanayin malamin lissafi ne, a makaranta a kasar tasu, ya shaidawa muryar Amurka dalilin sa na barin Sudan ta Kudu.

Yace ya bar garin Yei, ne inda suke, domin kullun ana cikin harbe-harbe da kwashe kayan jama’a, Kana mata ayi musu fyade, yace idan anyi miki fyade ma wata sa’a sai a kwace kayan dake jikin ki, a barki huntuwa, idan kuma baki sa’a ba a kashe ki, ko bayan fyaden

Yace wadannan sune dalilan barin su kasar, majalisar dinkin duniya tace kusan kashi 86 na sabbin ‘yan gudun hijirar mata ne da yara.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG