Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Sace Ma'aikatan Lafiya A Somaliya


Hukumomi a kudancin Somaliya, na neman wasu mutane hudu masu aikin ba da rigakafin Polio, wadanda mayakan kungiyar al-Shabab su ka sace.

Mutanen, wadanda biyu masu bayar da rigakafin ne, biyu kuma direbobi, kuma dukkanninsu 'yan Somaliya ne, an sace su ne ranar Lahadi daura da garin Luuq, da ke yankin Gedo. An yi imanin ainihi suna aiki ne a wani shirin kungiyar lafiya ta duniya kafin hukumomin yankin su ka bukaci taimakonsu.

Mohammed Hussein Ganey, Ciyaman din Luuq, ya ce, "Mutane biyun na kan fadakar da mutane tare kuma tara yara saboda a basu rigakafin" lokacin da aka sace su.

Mutanen dai sanannu ne a birnin. Hukumomi sun ce suna kan kokarin ganin an maido da mutanen ba tare da wani lahani ba.

Kanar Deeq Abdi Khaliif, kwamandan sojojin Somaliya, a Luuq, ya ce ma'aikatan na cikin gidajensu ne ma lokacin da wasu 'yan bindiga su ka kutsa cikin gidajen suka tasa keyarsu karfi da yaji sannan suka saka su a mota zuwa wani lungu.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG