Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jam'iyyar Republican Ta Shirya Don Fara Babban Taronta Na Kasa


Wakilan babban taron jam’iyyar Republican na ta sauka a jihar North Carolina a wannan makon, inda saboda annobar coronavirus aka takaita adadin wadanda zasu halarci taron a zahiri da kuma wadanda za a gudanar ta yanar gizo.

A makon jiya, yan jam'iyyar Democrat sun zargi Trump da cewa, matakan da ya dauka dangane da annobar coronavirus da kuma zangar zangar adawa da wariyar launin fata, sun ta’azzara.

Binciken ra’ayoyin jama’a na nuni cewa, dan takararsu Joe Biden yanzu ya sha gaban Trump da maki tara.

Amma Trump, na da farin jini a tsakanin ‘yan Republican. Tsakanin Amurkawa kuma maki 42 cikin dari da ya ke da shi, ya dara na bara. Wakili daga jihar Kansas, Mike Kucklelman ya ce ya saurari taron na Democrat amma baiji wani abu sabo ba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG