Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amfani Da Jiragen Soja A Lokacin Zanga-zangar Amurka Bai Saba Doka Ba - Pentagon


Ma'aikatar Tsaron Amurka Ta Pentagon
Ma'aikatar Tsaron Amurka Ta Pentagon

Yin amfani da jiragen yakin zaratan sojojin Amurka a wasu birane 4 domin sanya ido akan zanga-zangar da aka yi a fadin kasar a farkon wannan shekara bai sabawa dokokin bincike da tattara bayanai na soji ba akan Amurkawa, a cewar wani rahoton ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon.

Binciken da Babbab Sifeton Sojin Sama ya gudanar, ya gano cewa an yi amfani da jiragen ne domin tattara bayanai akan yawan taron masu zanga-zanga, da yadda suke sintiri da kuma wuta da ake cinnawa, amma ba su sanya ido akan daidaikun jama’a ba.

Sakataren Tsaro Mark Esper ne ya ba da umarnin a gudanar da binciken, domin amsawa ga tambayoyin da suka bijiro a ma’aikatar da kuma majalisar dokoki, akan ko sojoji sun yi liken asirin Amurkawa da ya saba ka’ida a lokacin zanga-zangar da aka yi sanadiyyar mutuwar George Floyd.

Sakataren Tsaron Amurka Mark Esper
Sakataren Tsaron Amurka Mark Esper

Amfani da jiragen ya zo ne a yayin da Shugaba Donald Trump ya yi kiran da a dauki tsauraran matakan dakile zanga-zangar. Floyd bakar fata ne da ya mutu, bayan wani dan sanda farar fata ya danne masa wuya da gwiwar kafarsa tsawon mintuna.

An yi amfani da zaratan sojin Amurka domin taimakawa jami’an tsaro na jihohi a wasu birane da dama na kasar.

An yi amfani da jiragen na sintiri ne a wurare 4. Kuma a yayin da rahoton ya gano cewa ba inda aka saba dokar tattara bayanai, ya kuma ce ma’aikatar tsaro ba ta da wasu takamaiman dokoki na yin amfani da jirgin saman samfurin RS-26, kuma an yi kuskuren tunanin cewa jirgin ba na tattara bayanai ba ne.

Jami’in soja ne ke tuka jirgin, kuma akasari ana amfani da shi ne wajen ayukan yaki da fataucin miyagun kwayoyi da lokutan ibtila’i domin kiyasta barna, da kuma taimakawa wajen gano wadanda lamarin ya rutsa da su da dai sauran ayuka makamantansu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG