A jawabinsa na farko a fagen siyasar kasa, dan takarar mataimakin shugaban kasa Donald Trump, Sanata J.D. Vance, ya fita ya yi jawabi mai karfi da jan hankali.
“Mun gama shigo da ma’aikata daga kasashen waje. Za mu yi yaki don kare ‘yan kasar Amurka da kyawawan ayyukansu da kyakkyawan albashinsu."
Vance wanda ba sananne ba ne a Amurka, ya yi karatu a fitacciyar makarantar koyon aikin lauya ta Yale, ya kuma yi aikin soja na tsawon shekaru shida. An zabe shi zuwa Majalisar Dattijai inda ya yi aiki na kusan shekara daya da rabi.
Matarsa Usha Vance ce ta gabatar da shi
Tace, "An zabe shi don taimakawa wajen jagorantar kasarmu a lokacin da take fuskantar kalubale mafi girma a tarihin kasar. Ina yi ma dukan ku godiya bisa amanar da kuka ba shi.”
Daren Laraba wata dama ce ba kawai ga Vance don gabatar da kansa ga jama'ar Amurka ba, amma dama ce da zai
nuna kwarewar da ya ke da ita kan manufofinsa na ketare.
"Tare, za mu tabbatar da cewa mun hada hannu da abokan kawancenmu wajen daukar nauyin tabbatar da zaman lafiya a duniya, ba za a ci gaba da kashewa kasashen da ke cin bilis da kudin harajin Amurkawa."
Wakilai sun ce rashin gogewar Vance bai dame su ba. Kamar yadda Walter Goodwater wakilin Republican daga jihar Texas ya bayyana.
"Hakika abin da muke zaba a nan shi ne iya shugabanci, kuma ya nuna yana iya jagorancin kwarai, kuma ba kamar mu tsofaffin ba ne."
"Na ji dadi cewa, shi matashi ne kuma ana iya nuna mashi hanya, kuma yana sa Amurka a gaba, wanda hakan ya dace. Ina tsammanin a karkashin kulawar Trump, zai iya yin nisa sosai."
A jawabinshi, Dan Trump ya bayyana zabin da ke gaban masu jefa kuri'a.
"Zabi ne tsakanin mutanen da ke alfahari da Amurka da kuma mutanen da ke jin kunyar Amurka, kuma a karshe, zabi ne tsakanin Amurkaa karshe da sa Amurka a gaba."
Za a rufe taron da yammacin yau Alhamis tare da jawabin Dobald Trump na karbar takarar shugaban kasa na jam'iyyar Republican. Wannan ne jawabinsa na farko a bainar jama'a tun bayan da ya tsallake rijiya da baya a wani yunkurin kashe shi.
Dandalin Mu Tattauna