Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jajiberin Zabe: A Ina Donald Trump Da Kamala Harris Za Su Karkare Yakin Neman Zabe?


Donald Trump (Hagu) Kamala Harris (Dama)
Donald Trump (Hagu) Kamala Harris (Dama)

Tuni dai Amurkawa kimanin miliyan 77 sun riga sun kada kuri’a tun da wuri yayin da Harris da Trump suke kokarin jawo karin miliyoyin magoya kafin zaben na Talata.

Mataimakiyar Shugaban kasa kuma ‘yar takarar jam’iyyar Demcorat Kamala Harris za ta shafe yinin ranar Litinin a jihar Pennsylvania, wacce ake ganin kuri'unta na jiha 19 (Electoral College Votes) za sui ya nuna akalar wanda zai lashe zaben.

Harris za ta ziyarci wuraren ma’aikata a Allentown, sannan ta kammala da taro a Philadelphia wanda zai samu halartar mawakiya Lady Gaga da Oprah Winfrey.

Donald Trump an nasa bangaren, ya shirya taruka guda hudu a jihohi uku, inda zai fara da Raleigh a jihar North Carolina, sannan ya yada zango sau biyu a Pennsylvania, ya kuma gudanar da wani taro a Reading da Pittsburgh.

Tsohon shugaban kasa kuma dan takarar jam’iyyar Republican zai gama kammala yakin neman zabensa kamar yadda ya gama na farko da na biyu, da wani taro a daren Litinin a Grand Rapids, Michigan.

Tuni dai Amurkawa kimanin miliyan 77 sun riga sun kada kuri’a tun da wuri, amma Harris da Trump suna kokarin jawo karin miliyoyin magoya baya su fito a ranar Talata.

Nasarar Trump za ta sa ya zama shugaban kasa mai jiran gado na farko da aka tuhume shi kuma aka same shi da aikata manyan laifuka, bayan shari'arsa ta toshiyar baki a New York.

Wannan zai ba shi damar kawo karshen wasu bincike na gwamnatin tarayya da ake gudanarwa a kansa saboda iko da zai samu a matsayin na shugaban kasa.

Trump zai kuma zama shugaban kasa na biyu a tarihin da ya lashe zaben shugaban kasa ba a jere ba, bayan Grover Cleveland a karshen karni na 19.

Harris tana neman zama mace ta farko, Ba’amurkiyar Afirka ta farko kuma mutum na farko mai asalin jinin Asiya ta kudu da za ta kai ga Ofishin Shugaban Kasa, shekaru hudu bayan ta kafa irin wadannan shingayen a matsayin mataimakiyar shugaban kasa, inda ta zama mataimakiyar Shugaba Joe Biden.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG