Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jagoran juyin mulkin Mali ya ce an maido da aiki da kundin tsarin mulki


Kaftin Amadou Haya Sanogo, jagoran juyin mulkin Mali
Kaftin Amadou Haya Sanogo, jagoran juyin mulkin Mali

Jagoran juyin mulkin kasar Mali ya ce ya maido da aiki da kundin

Jagoran juyin mulkin kasar Mali ya ce ya maido da aiki da kundin tsarin mulkin kasar, ana saura kwana guda kafin cikar wa’adin kakaba takunkumin tattalin arziki mai tsanani, matukar ba a maido da aiki da kundin tsarin mulki ba.

Yayin wani taron manema labaran da ya kira a kusa da Bamako, babban birnin kasar a yau Lahadi, Kaftin Amadou Sanogo ya karanta wani dan gajeren jawabi inda ya ce ya maido da kundin tsarin mulkin kasar, wanda aka amince da shi a 1992.

Ya kuma ce an maido da magudanan harkokin kasar kuma ya sha alwashin maido da iko ga fararen hula. To saidi kuma, jagoran juyin mulkin bai bayyana jadawalin sabon zaben ba.

Kungiyar cigaban tattalin arzikin kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS a takaice) ta yi barazanar kakaba tsattsauran takunkumin tattalin arziki zuwa gobe Litini muddun ba a maido da ragamar iko ga fararen kaya ba.

A halin da ake ciki kuma, shaidu a arewacin Mali sun gaya wa Muryar Amurka cewa ‘yan tawayen Asbinawa sun isa birnin Timbuktu, kuma ana ta gwabza yaki da wasoso a wannan gari na tarihi.

XS
SM
MD
LG