Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yan tawaye sun kwace arewacin kasar Mali


Sojojin suna sintiri a sansanin shugaban juyin mulki Amadou Sanogo
Sojojin suna sintiri a sansanin shugaban juyin mulki Amadou Sanogo

Shugabannin kasashen yammacin Afrika suna shirin gudanar da taron koli yau Litinin a kasar Senegal kan sauyin lamura da ake ci gaba da samu a kasar Mali

Shugabannin kasashen yammacin Afrika suna shirin gudanar da taron koli yau Litinin a kasar Senegal kan sauyin lamura da ake ci gaba da samu a kasar Mali inda sojoji suka kwace iko a wani juyin mulki da suka yi watan jiya.

Shugabannin juyin mulkin da kuma mayakan azbinawa dake tada kayar baya da nufin neman ‘yancin cin gashin kai a yankinsu dake arewacin Mali suna neman karfin iko a kasar.

Yan tawayen sun kwace garuruwan arewacin kasar da suka hada da birnin Timbuktu mai cike da tarihi, birni na karshe mafi girma dake karkashin ikon sojojin.

Jiya Lahadi,Shugaban juyin mulkin kyaftin Amadou Sanogo ya sanar da maido da kundin tsarin mulkin kasar da aka shata a shekara ta dubu dari tara da casa’in da biyu. Ya kuma amince da mika kusan dukan iko ga zababbiyar gwamnatin farin kaya. Sai dai bai fadi lokacin da za a gudanar da zabe ba.

Sanarwar tazo kwana daya kafin kungiyar hadin kan tattalin arzikin kasashen nahiyar Afrika-ECOWAS, ta sanar da takunkumin tattalin arziki mai tsauri muddar sojojin basu maida mulkin farin kaya ba.

Sojojin sun kwace mulki daga shugaba Amadou Toure da aka zaba karkashin tsarin damokaradiya a ranar 22 ga watan Maris. Suna zargin shi da gaza samar da isassun kayan aiki ga sojojin da zasu iya shawo kan tada kayar baya da azbinawan ke yi.

XS
SM
MD
LG