Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AU Tabi Sawun ECOWAS A Azawa Mali Takunkumi


Wakilan kasashe dake kungiyar ECOWAS a taron koli da suka yi a Dakar, Senegal.
Wakilan kasashe dake kungiyar ECOWAS a taron koli da suka yi a Dakar, Senegal.

Tarayyar Afirka tabi sawun kungiyar ECOWAS wajen azawa shugabannin juyin mulki a Mali takunkumi hana su tafiye tafiye da kuma kan kadarorinsu.

A jiya talata majalisar tsaro da zaman lafiya ta tarayyar Afirkan, ta bada umurnin kakabawa Malin takunkumi a fadin nahiyar baki daya, bayan wani zama da tayi na sa’o’I uku. Kwamishinan majalisar Ramtane Lamamra ne ya bada sanarwar kan matakan da suka dauka

Majalisar inganta zaman lafiya da tsaro ba tareda bata wani lokaci ba ta dauki daidaikun matakai da suka hada da takunkunmin hana tafiye tafiye, da kuma daurin talala kan kadarori na shugaban sojojijinda suka yi juyin mulki, da kuma akan duk mutuminda ko kungiyoyi da suke taimakawa ta ko wani hanya wajen dorewar wan tsari da ya sabawa tsarin mulki.

Lamamra yace majalisar tabbatarda zaman lafiya da tsaron ta kuma goyi bayan matakinda kungiyar raya tattalin arzikin kasashe dake yammacin Afirka watau ECOWAS ta dauka na saka rundunar mayaka na musamman dake karkashinta cikin shirin ko ta kwana. Majalisar ba tareda bata wani lokaci ba ta dakatarda Mali daga tarayyar,bayanda sojoji a kasar suka ayyana juyin mulki ranar 21 ga watan jiya a Bamako. Amma a lokacin, shugaba majalisar Jin Ping yace za a baiwa sojojin wata shida su sake maido da mulkin demokuradiyya, kamin a azawa kasar Takunkumi.

Amma ana ganin Wan nan mataki da kungiyar ta dauka na bin sawun ECOWAS wajen azawa Mali takunkumi cikin gaggawa ya biyo bayan suka da tarayyar ta sha saboda sanyin jiki da ta nuna bayan bore da jama’ar wasu kasashe dake arewacin Afirka suka tayar a bara.

Bayan taron na jiya talata, Kwmaishina Lamamra ya gayawa manem labarai cewa ya sami tabbacin cewa shugaba Amadou Toumani Toure na cikin koshin lafiya a wani wuri da ba a bayyana ba,a wajen birnin Bamako, kuma har yana samu yana tuntubar shugaban kasar Ivory Coast, Allassane Ouatara.

“Ina ji yana tuntubar wasu gwamnatoci. Yayi magana da shugaba Allasanne Ouattara ta woyar tarho, kuma na hakikance babu abinda ya taba lafiyarsa, yana walwala, kuma yana goyon bayan shawarwari da taron koli na musmaman na ECOWAS ta yanke kan rikicin kasar”.

Ranar litinin kungiyar ECOWAS mai wakilai 15 da suka hada da kasashe dake makwabtaka da Malin suka yi wani taron koli na musamman inda suka azawa kasar takunkumi, suka da rufe kan iyakokinta da kuma account din kasar na babban bankin yankin baki daya. Ana sa ran takunkumin ba tareda wani bata lokaci ba zai sanya kasar cikin matsi sosai, ganin ta dogara ne dungurum kan hanyoyin doron kasa wajen jigilar mai zuwa cikin kasar.

XS
SM
MD
LG